Drogba ya yi murabus daga bugawa Ivory Coast wasa

Hakkin mallakar hoto
Image caption Drogba ya shafe shekaru 8 yana rike da kambun kaftin din kungiyar Elephants na Ivory Coast

Dan wasan kasar Ivory Coast Didier Drogba ya sanar da yin murabus daga bugawa kasar sa wasanni.

Drogba ya ce yana matukar alfahari da tsawon shekaru 12 da ya yi yana bugawa kasar sa wasanni inda ya ce hakan ya ba shi damar bada gudummuwa ga kasar sa.

Dan wasan wanda shi ke rike da kambum kaftin din na kungiyar Elephants har na tsawon shekaru 8 ya taka muhimmiyar rawa wajen daukaka martabar kasar sa a fagen wasanni, inda ya bugawa kasar wasanni har sau uku a gasar cin kofin duniya da kuma kaiwa ga matakin karshe har sau biyu na gasar cin kofin nahiyar Afrika.

Drogba ya jinjinawa magoya bayan kungiyar ta Elephants saboda kaunar da suka nuna masa tare kuma da jinjinawa takwarorin sa na kungiyar bisa goyon bayan da suka ba shi.