Sammy ya zabi bugawa Nigeria kwallo

Sammy Ameobi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sammy yana son ya buga wa Super Eagles kwallo

Dan kwallon Newcastle Sammy Ameobi ya yanke shawarar bugawa Nigeria kwallo duk lokacin da aka bukace shi.

Sammy, mai shekaru 22 dan uwan Shola Ameobi dan wasan Super Eagles, ya wakilci Ingila inda ya buga mata kwallon kafa ta matasa 'yan kasa da shekaru 21.

Dan wasan ya sanar da BBC ce wa "Bai bata lokaci ba wajen yanke hukuncin amincewa ya bugawa Nigeriya wasa ba".

Ya kuma kara da ce wa "Ya kalli wasan Shola a gasar kofin duniya, kuma buga babbar gasa irin wannan na karawa dan kwallo kwarin gwiwa".

Sammy Ameobi ya fara bugawa Newcastle wasa ne a watan Mayun shekarar 2011, an kuma bada shi aro ga Middlesbrough a tsakiyar kakar wasan 2012-13.