Man United na zawarcin Vermaelen

Thomas Vermaelen Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Wenger yafi kaunar ganin dan wasan ya bar buga Premier

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce kulob din Manchester United na daya daga cikin wadanda suke zawarcin kyaftin din kungiyar Thomas Vermaelen.

Dan wasan mai shekaru 27 da haihuwa ya buga wa Arsenal wasanni 14 a kakar bara, kuma kungiyoyi da dama na zawarcinsa.

Wenger bai fadi kudin da ake kokarin sayen dan wasan ba, sai dai ya ce yafi kaunar dan kwallon ya koma buga tamaula a wata kasar.

Kocin Arsenal ya taba fada a baya cewa Vermaelen, wanda yana cikin tawagar 'yan wasan Belgium a gasar kofin duniya yaji rauni kuma zai iya barin kulob din.

Vermaelen ya koma Arsenal daga Ajax a watan Yulin 2009, daga baya ya zama fitaccen dan wasa da ake damawa da shi a kungiyar koda yaushe.