Luiz ya mance da gasar kofin Duniya

David Luiz Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dan wasan ya ce zai saka kaimi domin nuna kwarewarsa

David Luiz ya ce ya farfado daga rashin kokarin da suka yi a gasar kofin duniya da akayi a Brazil, lokacin da PSG ta gabatar da shi a gaban magoya bayan kulob din.

Dan kwallon mai tsaron baya ya bar kulob din Chelsea kan kudi fan miliyan 40, kuma shi ne kyaftin a wasan da Jamus da doke Brazil da ci 7-1 a gasar cin kofin duniya da aka kammala.

Luiz, mai shekaru 27 da haihuwa, ya kara da cewa "Tun da Brazil ta kai wasan daf da na kusa da karshe, babu dalilin tantamar kwarewarsa a tamaula".

"Tuni na mance da yadda wasa ya juya mana baya a gasar cin kofin Duniya, yanzu a shirye nake na taka wasa da zai daga martabar PSG".

Dan wasan mai tsaron baya mafi tsada da aka saya a bana, wanda ke iya buga wasan tsakiya, wannan ne karon farko da ya gana da 'yan jaridu tun lokacin da ya koma Faransa wasa.

Luiz ya koma Blues daga Benfica kan kudi sama da fan miliyan 21 a watan Janairun 2011, inda ya kuma buga wasanni 143.