Newcastle United ta dauki 'yan wasa 2

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An saida Lascelles da kuma Darlow ba a son ran Kulob dinsu ba

Newcastle United ta tabbatar da daukar dan wasan bayan Nottingham Forest Jamaal Lascelles da kuma mai tsaron gida Karl Darlow akan kudin da ba a bayyana ba.

Za a tura 'Yan wasan Ingilan biyu a matsayin aro ga Forest a kakar wasannin 2014-2015.

Manajan Newcastle Alan Pardewa ya kwatanta daukar 'yan wasan biyu daga Forest a matsayin wani juyin mulki na zahiri da suka yi wajen daukar zaratan 'yan wasan Ingilan biyu.

Sai dai Manajan Forest Stuart Pearce ya ce an saida Lascelles da kuma Darlow ba a son ransa ba.