Afellay zai koma Olympiakos wasa aro

Ibrahim Afellay Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Saura shekara daYA kwantiraginsa da Barca ta ka re

Dan kwallon Barcelona mai wasan tsakiya Ibrahim Afellay, zai koma kulob din Girka Olympiakos kwallo aro har zuwa karshen kakar wasan bana.

Dan wasan mai shekaru 28 da hauhuwa, ya koma kwallo Barca ne daga kulob din PSV Eindhoven a Disambar 2010 ya kuma buga wasanni 35.

Dan kwallon Netherland wanda ya buga mata wasanni 44, baya samun buga wasa a Barca a kai a kai sakamakon rauni da ya ji a bayansa a watan Satumbar 2011.

Afellay ya buga gasar wasan bana a kungiyar Schalke, kuma saura shekara guda kwantiraginsa ya kare da Barcelona.