Vermaelen ya kammala komawa Barca

Thomas Vermaelen Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya rattaba kwantiragin shekaru biyar a Barca

Kyaftin din Arsenal mai tsaron baya Thomas Vermaelen, ya kammala komawa kulob din Barcelona kan kwantiragin shekaru biyar akan kudi fan miliyan 15.

Dan kwallon Belgium mai shekaru 28 da haihuwa, bayan an duba lafiyarsa a Barca ya kuma amince zai ci gaba da wasa a kulob din har karshen kakar wasa na 2018-19.

Vermaelen, ya koma kungiyar Arsenal ne daga Ajax kan kudi fan miliyan 10 a shekarar 2009 ya kuma buga wasanni 150.

Tun farko Manchester United ce ta bukaci daukar dan kwallon da tayin mikawa Arsenal dan wasa mai tsaron baya, Amma Wenger ya gwammace Vermaelen ya bar gasar Premier.

Vermaelen ya yi fama da jinyar rauni a bara, dalilin da yasa Arsene Wenger ya dinga amfani da Per Mertesacker da Laurent Koscielny a maimakonsa.