Nasri zai bar buga wa Faransa tamaula

Samir Nasri Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya ce baya samun jituwa tsaninsa da koci da 'yan Jaridu

Dan kwallon Manchester City Samir Nasir, ya ce zai daina buga wa kasar France wasa, bayan da suka sami rashin jitiwa tsakaninsa da koci Didier Deschamps da 'yan jaridun kasar.

Kocin tawagar kasar Faransa Deschamps, bai gayyaci Nasir cikin tawagar 'yan wasan kasar da suka halarci gasar kofin duniya da aka kammala a Brazil ba.

Deschamps ya dauki matakin shari'a kan budurwar Nasri Anara Atanes, bisa wasu kalamai da tayi a Twitter kan rashin gayyatar dan kwallon zuwa tawagar da ta wakilci Faransa a gasar .

Nasri ya ce "idan har kocin ne yake horas da tawagar kasar, ban ga dalilin da zan iya buga wasa ba, ba ni da kwanciyar hankali idan ina wasa, kuma duk lokacin da aka gayyace ni sai an sami matsala".

Dan wasan ya buga wa kasarsa wasanni 41, shi ma tsohon kocin Faransa Raymond Domenech, bai gayyaci dan kwallon zuwa buga gasar kofin Duniya ba a shekarar 2010.

Sai dai Nasri ya wakilci kasarsa a gasar cin kofin Nahiyar Turai a shekarar 2012, kafin Faransa ta dakatar da shi buga wasanni uku.