Drogba ya ji rauni a wasan Chelsea

Didier Drogba Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dan wasan zai buga wa Chelsea kwallo a gasar bana

Kulob din Chelsea ya doke Ferencvaros da ci 2-1 a wasan atisayen da suka kara, inda Didier Drogba ya ji rauni tun kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Dan kwallon Ivory Coast ya fara buga wa kulob din wasan farko tun lokacin da ya koma kungiyar, inda aka duba masa agara bayan da Zoltan Gera ya zura wa Chelsea kwallo a raga.

Duk da musanya Drogba da aka yi a karawar, Chelsea ta farke kwallonta ta hannun Ramires.

Sabon dan kwallon da Chelsea ta sayo Fabregas ne ya kara kwallo ta biyu a raga ya rage mintuna 10 a tashi wasa.

Ga sunayen 'yan kwallon da suka buga wa Chelsea wasa:

Cech (Schwarzer 45); Azpilicueta (Moses 66), Zouma, Christensen (Cahill 45), Filipe Luis (Ivanovic 45); Ramires (Hazard 60), Mikel (Matic 60); Schurrle (Salah 45), Willian (Fabregas 45), Torres (Diego Costa 45); Drogba (Oscar 28 (Ake 78)).

Ga sunayen 'yan kwallon da suka buga wa Ferencvaros wasa:

Dibusz, Nalepa, Mateos, Pavlovic, Bonig, D Nagy, Gyomber, Csukics, Busai, Gera, Bode.