Za'a ba Fiorentina aron Marko Marin

Marko Marin Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A bara kulob din Sevilla ya buga wa kwallo aro

Dan kwallon Chelsea mai wasan tsakiya Marko Marin na daf da koma wa kulob din Fiorentina wasa aro, tsawon shekaru da dama.

Kulob din Fiorentina da ke Italiya ya sanar ta shafin Twitter ce wa dan kwallon mai shekaru 25 da haihuwa dan wasan Jamus ya isa kungiyar, har ma ana duba lafiyarsa.

Sau shida kacal Marin ya buga wa Chelsea wasan Premier tun lokacin da ya koma kulob din kan kudi fan miliyan bakwai daga Werder Breme a shekarar 2012.

Marin ya buga wa Sevilla wasanni 18 aro, wanda ya taimakawa kungiyar lashe kofin Europa League da suka doke Benfika, inda ya shiga wasa a sauyin dan kwallo.

Komawarsa Florence zai kara hura wutar jita-jitar cewa dan kwallon Colombian Juan Cuadrado zai bar kungiyar a bana.