Manchester City ta dauko Mangala

Eliaquim Mangala
Image caption Dan kwallo na shida da City ta dauko a bana

Kungiyar Manchester City ta kammala daukar dan wasan Porto kan kudi da ake hasashen zai kai fan miliyan 32 akan kwantiragin shekaru biyar.

Dan wasan mai shekaru 23 da haihuwa dan kwallon Faransa, tun a watan Janairun bana ne City ta yi kokarin dauko shi.

Kocin City Manuel Pellegrini ya ce "Dan kwallon yana da kwarewar da zai zama fitatcen dan wasa mai tsaron baya a Nahiyar Turai".

Mangala yana cikin tawagar 'yan kwallon Faransa a gasar cin kofin Duniya da aka kammala a Brazil, sai dai bai buga wasa ba.

Dan wasan ya zamo na shida da City ta dauko a bana, kuma na biyu daga kulub din Porto, bayan dan kwallon Brazil Fernando da aka saya kan kudi fan miliyan 12.