Rodriguez zai fara yi wa Madrid wasa

James Rodriguez Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sabbin 'yan wasan za su fara buga wa Madrid wasa ranar Talata

Sabbin 'yan wasan da kulob din Real Madrid ya dauko a bana, James Rodriguez da Toni Kroos, za su buga wa kungiyar wasansu na farko a karawar da za tayi da Sevilla a wasan Super Cup ranar Talata.

Rodriguez, wanda ya lashe takalmin zinare a gasar kofin duniya da aka kammala a Brazil, inda ya zura kwallaye shida a raga, ya koma Madrid daga kulob din Monaco.

Shi ma dan kwallon Jamus wanda yake tawagar kasar da suka lashe kofin duniya Kroos, zai fara buga wa Real Madrid tamaula a ranar.

Karawar da ta kunshi kungiyoyi biyu daga Spaniya, shi ne lokacin da dan kwallon Cardiff Bale zai buga wasan a garinsu sanye da taguwar Madrid.

Shi ma tsohon dan kwallon Manchester United Cristiano Ronaldo, yana cikin 'yan wasa 22 da za su buga karawar.

Rabon Madrid ta dauki kofin Super Cup tun shekarar 2002, kuma za su fafata da Sevilla a birnin Cardiff.

Karawar za ta bai wa kocin Madrid Ancelotti damar lashe kofin farko daga cikin kofuna shida da kulob din yake fatan lashe wa a bana.