Silva ya sabunta kwantiraginsa da City

David Silva Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan kwallo na uku da ya sabunta kwantiragi da City

Dan kwallon Spain David Silva ya tsawaita kwantiraginsa da kulob din Manchester City zakarar kofin Premier Ingila.

Dan wasan mai shekaru 28 da haihuwa, ya koma City ne kan kudi fan miliyan 24 daga Valencia a watan Yulin 2010.

Silva ya zura kwallaye takwas daga cikin wasanni 40 da ya buga, ya kuma taimakawa City lashe kofin Premier a bara da kofin Capital One.

Yana kuma cikin 'yan wasan kulob din da suka dauki kofin Premier a kakar wasan 2011-12, da kuma kofin FA a shekarar 2010-11.

Shi ne dan kwallo na uku da ya sabunta kwantiraginsa da City a bana, bayan Samir Nasri da mai tsaron baya Aleksandar Kolarov.