NFF ta sabunta kwantiraginta da Keshi

Stephen Keshi
Image caption NFF ta sabunta kwantiraginta da Stephen Keshi

Hukumar gudanar da wasan kwallon kafa ta Nigeria ta ce ta sabunta kwantiraginta da koci Stephen Keshi, domin ya ci gaba da horas da Super Eagles.

Hukumar NFF ta sanar da daukar kocin ne ranar Talata, sai dai ba ta bayyana shekaru nawa zai yi ba da albashin da za a ba shi ba, a tsawon aikin da zai yi.

A dan karamin jawabi da hukumar ta sanar ta ce kwamitin amintattu na NFF na fatan kwammala kulla yarjejeniya tsakaninta da kocin cikin kwanaki masu zuwa.

Keshi ya jagoranci Najeriya lashe kofin Nahiyar Afirka a shekarar 2013, ya kuma kai kasar wasannin zagaye na biyu a gasar kofin Duniya da aka kammala a Brazil.

Ya yi murabus daga kocin tawagar 'yan wasan Najeriya kwana daya da lashe kofin Afirka a bara, kafin daga baya aka lallashe shi ya kuma sake karbar aikin kocin kasar