Hoddle zai taimakawa Rednaff a QPR

Glenn Hoddle Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hodlles zai taimakawa Rednaff horas da QPR

Kulob din Queens Park Rangers ya dauko tsohon kocin Ingila Glenn Hoddle a matsayin mataimakin Harry Redknapp.

Kocin mai shekaru 56 da haihuwa, zai yi aike ne tare da masu horar da kungiyar da suka hada da Joe Jordan da Kevin Bond.

Hoddles ya ce "Ina sha'awar horas da 'yan kwallo a koda yaushe, na kagu a gabatar dani ga 'yan wasa na fara aiki da su".

Tsohon kocin Swindon da Chelsea da Tottenham da Southampton, wanda ya horas da Ingila tsakanin shekarun 1996 zuwa 1999, ya jagoranci kungiya ta karshe Wolves wacce ya bari a watan Yulin 2006.

Hoddles ya bugawa Tottenham wasanni tsawon shekaru 13, kafin ya koma Monaco a shekarar 1987, ya komo Swindon ta Ingila a matsayin koci kuma dan wasa a shekarar 1991. Shekaru biyu kuma ya koma Chelsea.