Kano Pillars ta doke Enugu Rangers 3-2

Kano Pillars Hakkin mallakar hoto Kano Pillars Web Page
Image caption Kano Pillars har yanzu tana matsayi na daya a teburi

Kungiyar Kano Pillars ta doke Enugu Rangers da ci 3-2 a gasar cin kofin Premier wasannin mako na 23 da suka kara ranar Laraba.

Rangers ce ta fara zura wa Pillars kwallo sakwan biyar da fara wasa ta hannaun dan wasanta Christian Obiazor, kafin daga baya Rabi'u Ali ya farke mata.

Rangers dai ce ta kara kwallo ta biyu a ragar Pillars kafin Rabi'u Ali ya kara farkewa ya kuma zura kwallo ta uku ya rage mintoci a tashi wasa.

Sauran sakamakon wasanni sun hada da Kaduna United da ta doke Akwa United da ci daya mai ban haushi, ita ma Elkanemi Warriors ta doke Taraba United da ci daya na nema.

Karawa tsakanin Sharks da Heatrland an tashi wasa kunnen doki, inda Enyimba ta sami nasara a kan Warri Wolves da ci biyu da nema.

Har yanzu Kano Pillars ce take matsayi na daya a teburi da maki 40, bayan buga wasannin mako na 23, Nasarawa United na matsayi na biyu da maki 38, sai Dolphins mai maki 37 a matsayi na uku.

Ga sakamakon wasannin mako na 23:

Kano Pillars 3 vs 2 Enugu Rangers Enyimba 2 vs 0 Warri Wolves Kaduna United 1 vs 0 Akwa United Nembe City 1 vs 0 Abia Warriors Giwa FC 1 vs 0 Sunshine Stars Nasarawa United 2 vs 1 Bayelsa United Sharks 1 vs 1 Heartland FC El-Kanemi Warriors 1 vs 0 Taraba FC Dolphins FC 2 vs 0 Crown FC Gombe United 3 vs 1 Lobi Stars