Liverpool ta amince da farashin Moreno

Alberto Moreno Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan kwallo na takwas da Liverpool ta dauko a bana

Kulob din Liverpool ya amince da farashin dan kwallon Sevilla Alberto Moreno, da aka yi masa kudi kan fan miliyan 12.

Dan wasan Spaniya mai shekaru 22 da haihuwa, zai halarci Merseyside cikin makwonnan domin duba lafiyarsa.

Sai dai dan kwallon Liverpool Martin Kelly, mai shekaru 24 da haihuwa zai koma Crystal Palace kan kudi kusan fan miliyan 2.

Moreno ya zamo dan wasa na takwas da Liverpool ta dauko a bana, zai kuma fafata da Jose Enrique a gurbin buga mai tsaron baya ta bangaren hagu.

Cikin 'yan kwallon da kulob din ya dauko sun hada da Rickie Lambert da Adam Lallana da Dejan Lovren da Lazar Markovic da Emre Can da kuma Javier Manquillo da ya koma wasa aro daga Atletico Madrid.

Liverpool ta kuma dauko Divock Origi kan kudi fan miliyan 10 daga Lille, amma ta bar shi a kungiyar ya buga mata kwallo aro zuwa karshen kakar bana.