An nada Rooney kyaftin din Man United

wayne rooney Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rooney sabon Kyaftin din Manchester United

Kulob din Manchester United da ke Ingila ya nada Wayne Rooney, a matsayin sabon kyaftin din kungiyar.

Dan wasan Ingila mai shekaru 28 da haihuwa, ya maye gurbin Nemanja Vidic wanda ya bar kulob din ya koma Inter Milan na Italiya.

United ta kuma nada Darren Fletcher a matsayin mataimakin kyaftin din kungiyar.

Rooney ya ce "Yana farin cikin karbar wannan mukamin, sannan ya gode wa sabon kocin da ya yi amanna da cewar zai iya jagorantar 'yan kwallon".

United ta tabbatar wa da Rooney mukamin ne bayan tashi daga wasan sada zumunci da suka doke Valencia da ci 2-1 ranar Talata.

Rooney ya lashe kofunan Premier biyar da United da kuma kofin zakarun Turai a shekarar 2008 da kungiyar.