Van Gaal ya fara da nasara a Old Trafford

Louis van Gaal Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin ya fara wasa da kafar dama a Old Trafford

Sabon kocin Manchester United Louis van Gaal, ya lashe wasan farko a Old Trafford, bayan da ya jagoranci kungiyar da ta doke Valencia da ci 2-1 a wasan sada zumunci ranar Talata.

Marouane Fellaini dan wasan Belgium da aka dauko daga Everton ne ya kara kwallo ta biyu a ragar Valencia, nan take magoya bayan United suka barke da sowa da tafi.

Kocin Valencia Nuno Espirito Santo ya yi ta zarya a bakin filin wasa, shi kuwa Van Gaal ya ci gaba da zamansa a benci, bai ma miki tsaye don taya 'yan wasa murnar zura kwallo da Darren Fletcher ya yi da farke kwallon da Valencia ta yi.

United za ta fara gasar wasan Premier bana da Swansea ranar Asabar.

Ga sunayen 'yan wasan da suka buga wa United kwallo:

De Gea, James, Jones, Smalling, Blackett, Young, Fletcher, Herrera, Mata, Rooney, Hernandez. Subs: Amos, Cleverley, Kagawa, Fellaini, Lingard, Michael Keane, Januzaj.

Ga sunayen 'yan wasan da suka buga wa Valencia kwallo:

Diego Alves, Barragan, Vezo, Otamendi, Gaya, Parejo, Javi Fuego, Gomes, Feghouli, Alcacer, Rodrigo. Subs: Yoel, Piatti, Joao Pereira, De Paul, Guardado, Orban, Mustafi, Vinicius Araujo, Robert, Carles Gil, Domenech Jaume.