Kofin Duniya: Nigeria ta casa Ingila 2-1

Image caption Najeriya ta kai wasan dab da na kusa da karshe, inda za ta kara da New Zealand ranar Lahadi.

Najeriya ta doke Ingila da ci 2-1 a gasar cin kofin duniya na kwallon kafa ta mata 'yan kasa da shekaru 20 da ake yi a Canada.

Ingila ce ta fara cin Najeriya a minti biyar da fara wasa ta hannun N. Parris, kafin Ayila ta rama wa Najeriyar a minti na 41.

Ingila ta zubar da bugun fanaretin da ta samu, yayin da Najeriya ta ci wanda ta samu a minti na 59, inda Oshoala ta ci.

Najeriya ta kasance ta farko a rukuninsu na uku, Group C da maki bakwai.

A daya wasan rukunin kuma, Korea ta Kudu ta yi nasara a kan Mexico, ita ma da 2-1.

Korea ta Kudu mai maki hudu ta biyu, za ta yi wasan dab da na kusa da karshe da Faransa, ranar Lahadi.

Ingila ta uku da maki biyu da Mexico ta hudu a rukunin ita ma da maki biyu, sun fice daga gasar.