Scholes: 'van Gaal dan baiwa ne'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Manchester United na bukatar daukan sababbin 'yan wasa don tinkarar gasar Premier.

Tsohon dan wasan Manchester United Paul Scholes ya bayyana sabon kocin kulob din Louis van Gaal a matsayin dan baiwa wanda zai iya dawo da martabar kungiyar.

Manchester United wacce ta zama zakara a Gasar kwararru ta 2012-13, ta kammala Gasar bara a mataki na 7 lamarin da ya sa aka sallami kocin kulob din David Moyes cikin watan Afrilu bayan ya yi aikin watanni 8 kacal.

Scholes, mai shekaru 36, wanda ya koma United a matsayin mai bada shawara bayan sallamar Moyes, ya ce akwai bukatar Manchester United ta dauki sababbin 'yan wasa.

Tsohon dan wasan ya shaida wa jaridar Independent cewa, "Ba bu tantama dole ne 'yan wasan United su zage dantse a bana ko kuma su fuskanci kalubale a gasar Premier.