'Ban karbi aikin horas da Kenya ba'

Bobby Williamson Hakkin mallakar hoto Andy Gooch
Image caption Kocin ya ce zai dawo da tagomashin Gor Mahia a Cecafa

Kocin kulob din Gor Mahia Bobby Williamson ya ce bai karbi kwantiragin horas da tawagar 'yan wasan kwallon Kenya ba, kamar yadda a ke ta yadawa a baya.

Tsohon kocin Uganda ya kuma karyata rashin jituwa da ke tsakaninsa da hukumar kwallon ta Kenya ya taimakada aka cire kulob dinsa Gor Mahia daga gasar cin kofin Cecafa da Rwanda ke karbar bakunci.

Gor Mahia ta tashi wasa 2-2 da kulob din APR, karawar da ya kamata ta lashe wasan don ci samun tikitin kai wa zagayen wasan gaba.

Kulob din Vital'O ta Burundi mai rike da kofin bara, ita ma ba ta kai ga ci ba, saboda anyi waje da ita.

Williamson ya ce ya mai da hankalinsa ga kungiyar Gor Mahia, sai dai har yanzu mahukuntan Kenya ba su ce komai ba.