Liverpool ta doke Southampton 2-1

Daniel Sturridge goal Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Liverpool ta fara gasar Premier bana da kafar dama

Liverpool ta doke kulob din Southampton da ci 2-1 a gasar cin kofin Premier bana da suka kara a filin wasa na Anfield.

Raheem Sterling ne ya fara zura kwallo a ragar Southampton minti na 23 da fara wasa, bayan da ya samu kwallo ta hannun abokin wasansa Jordan Henderson.

Southampton ta farke kwallonta ta hannun Nathaniel Clyne a minti na 11 da dawo wa daga hutun rabin lokaci bayan da suka yi bani in baka tsakaninsa da Dusan Tadic.

Daniel Sturridge ne ya zura kwallo ta biyu da ya bai wa Liverpool damar samun maki uku a minti na 73, bayan da ya tsinci kwallon da Sterling ya sa mata kai.

A bara Liverpool ta kare a matsayi na biyu da maki 84 a teburi, inda Southampton ta karkare da maki 56 a matsayi na takwas.