AFCON: Rwanda za ta daukaka kara

CAF Cup of Nation
Image caption Rwanda za ta daukaka karar ne a kotun daukaka karar wasanni ta Duniya

Kasar Rwanda za ta daukaka kara kan hukuncin da CAF ta yanke na korarta da ta yi daga shiga wasannin neman tikitin zuwa gasar cin kofin Nahiyar Afirka na badi.

CAF ta kori Rwanda ranar Lahadi ne daga shiga wasannin bisa samunta da laifin yin amfani da dan kwallo da takardunsa da kuma shekarunsa suka banbanta a passport dinsa.

Rwanda ta sanarwa da BBC cewa za ta daukaka karar ne a kotun daukaka karar wasanni ta Duniya kan hukuncin da aka yanke mata.

Tun farko Congo ce ta shigar da korafi wurin CAF ga me da cancantar dan kwallon Rwanda Birori Dady.