Chelsea ta doke Burnley da ci 3-1.

Chelsea win Burnley Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Chelsea ta fara gasar bana da kafar dama

Kulob din Chelsea ya doke sabuwar kungiyar Burnley wadda ta dawo gasar Premier bana da ci 3-1 har gida a gasar cin kofin Premier wasan farko.

Dan kwallon Burnley Scott Arfield ne ya fara zura kwallo a ragar Chelsea daga tazara mai nisa, nan take cikin kankanin lokaci Chelsea ta farke kwallo ta hannun Diego Costa.

Andre Schurrle ne ya kara kwallo ta biyu a ragar Burnley lokacin da ya samu tamaula daga Cesc Fabregas, kafin daga baya Branislav Ivanovic ya kara kwallo ta uku a raga.

Didier Drogba da ya shiga sauyin dan wasa a kurarren lokaci ya kusa zura kwallo a raga.

Chelsea za ta buga wasanta na biyu a Stamford Bridge, inda za ta karbi bakuncin Leicester City, wanda Burnley za ta ziyarci kulob din Swansea ranar Asabar.