Wenger: Za mu kare martabarmu a Uefa

Arsene Wenger Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kocin na fatan Arsenal za ta lashe kofin zakarun Turai a bana

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce abu mafi mahimmaci a kulob din shi ne kare martabarsa a gasar cin kofin zakarun Turai ba kudin da zai samu ba.

Gunners wadda ta halarci gasar cin kofin zakarun Turai shekaru 16 a jere, za ta fafata da Besiktas ranar Talata a wasan cike gurbin shiga gasar.

Wenger ya ce "Hakika ana samun kudi a gasar, amma mun fi kaunar kafsawa a gagarumar gasa tare da zakakuren kungiyoyi".

Idan Arsenal ta samu tikitin shiga gasar zakarun Turan, za a ba ta kudi da zai kai sama da fan miliyan shida da rabi, da kuma karin sama da fan miliyan biyu a duk wasannin rukuni a matsayin kudin kallon wasan kungiyar.

Arsenal wadda ta kare a matsayi na hudu a teburin Premier bara, ta dauko Alexis Sanchez daga kungiyar Barcelona kan kudi fan miliyan 35 a bana.

Arsenal za ta karbi bakuncin Besiktas a karawa ta biyu ranar Laraba 27 ga watan Agusta.