Keshi: 'Ba zan koma aiki ba sai.....

Stephen Keshi
Image caption Keshi ya ce sama da kasashe bakwai ke zawarcinsa

Stephen Keshi ya ce ba zai karbi ragamar horas da tawagar Super Eagles ba har sai hukumar kwallon kafar Najeriya ta amince da bukatunsa.

Tun cikin watan Yuni hukumar kwallon kafar Nageriya ta amince za ta tsawaita kwantiragin kocin, amma rigimar da ke tsakanin korar da aka yiwa shugaban NFF Aminu Maigari ya kawo tsaiko.

Keshi ya bukaci a kara masa albashin da ake biyansa, inda yace shekaru biyu da rabi kenan yana karbar albashi babu kari.

Kocin ya jagoranci Najeriya zuwa lashe kofin Nahiyar Afirka a shekarar 2013, ya kuma kai Super Eagles wasan zagaye na biyu a gasar kofin Duniya da aka kammala a Brazil.

Nigeriya za ta kara da Congo a wasan neman tikin shiga gasar kofin Nahiyar Afirka ranar 5 ga watan Satumba.