An gayyato Aluko Super Eagles

Sone Aluko Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wannan ne karon farko da aka gayyaci dan wasan zuwa Super Eagles

Nigeria ta bayyana sunayen 'yan wasa 23 da za su bugawa Super Eagles karawar neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Afirka duk da ba ta da mai horaswa a yanzu.

Cikin tawagar 'yan kwallon da aka gayyata har da Sone Aluko, wanda zai fara bugawa Super Eagles tamaula a fafatawar da za tayi da Congo ranar 6 ga watan Satumba da Afirka ta kudu kwanaki hudu bayan wasan farko.

Hukumar kwallon kafar Najeriya ce ta zabo 'yan wasan, kuma hukumar na tattaunawa da Stephen Keshi don cigaba da rike kocin tawagar kasar.

Tun cikin watan Yuni suka fara tattaunawa tsakanin hukumar kwallon kafar Najeriya da Keshi don sabunta kwantiraginsa da Super Eagles wanda rikicin da ke NFF kan kokar Aminu Maigari daga mukaminsa ya kawo tsaiko.

Ga 'yan kwallon da Najeriya ta gayyato

Masu tsaron raga: Vincent Enyeama (Lille OSC, France), Austin Ejide (Hapoel Be'er Sheva, Israel), Chigozie Agbim (Gombe United)

Masu tsaron baya: Elderson Echiejile (Monaco FC, France), Juwon Oshaniwa (Ashdod FC, Israel), Efe Ambrose (Celtic FC, Scotland), Godfrey Oboabona (Rizespor , Turkey), Azubuike Egwuekwe (Warri Wolves), Kenneth Omeruo (Middlesbrough, England); Kunle Odunlami (Sunshine Stars)

Masu wasan tsakiya: John Mikel Obi (Chelsea FC, England), Ogenyi Onazi (SS Lazio, Italy), Ramon Azeez (Almeria FC, Spain), Joel Obi (Inter Milan, Italy), Nosa Igiebor (Real Betis, Spain), Sone Aluko (Hull City, England)

Masu wasan gaba: Ahmed Musa (CSKA Moscow, Russia), Emmanuel Emenike (Fenerbahce, Turkey), Chinedu Obasi (Schalke 04, Germany), Uche Nwofor (Heerenveen, Netherlands), Nnamdi Oduamadi (Crotone, Italy), Gbolahan Salami (Warri Wolves), Christian Osaguona (Enugu Rangers)