FIFA ta kori daukaka karar Barcelona

Barcelona Team Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Barcelona tace za ta kara daukaka kara kan hukuncin

Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA ta kori karar da Barcelona ta daukakakan hana ta sayen 'yan kwallo da zarar an rufe kasuwar bana har sai watan Janairun 2016.

FIFA ta hukunta Barca ne bisa samunta da aka yi da karya dokar musayar 'yan kwallo masu shekaru kasa da 18.

Tun farko hukumar ta dakatar da hukuncin ne bisa daukaka karar da Barcelona ta yi, wanda hakan ya ba ta damar sayo 'yan wasa ciki har da Luis Suarez a kakar bana.

Barcelona ta ce za ta kara daukaka kara a kotun daukaka karar wasanni ta Duniya.

Wannan hukuncin na FIFA zai fara aiki ne a badi, hakan na nufin kulob din zai iya dauko 'yan wasa kafin lokacin.

Barcelona ta ce hukuncin da aka yanke mata zai kashe karsashin bunkasa wasan matasa, musammam makarantar horon matasan 'yan kwallo mai suna La Masia, wadda ta fito da martabar kulob din wajen yaye 'yan kwallo da suke yin fice.

'Yan wasa kamar su Lionel Messi da Andres Iniesta da Xavi Hernandez, dukkansu daga makarantar suka fito.