United za ta biya Nani albashi a Lisbon

Luis Nani
Image caption United ce za ta biya shi albashi a Sporting Lisbon

Kulob din Manchester United zai biya Nani albashin da zai kusan fam miliyan biyar, tsawon lokacin da zai koma wasa aro a kungiyar Sporting Lisbon.

Dan wasan mai shekaru 27, zai koma buga tamaula a Portugal ne bisa yarje-jeniyar cinikin Marcos Rojo da zai koma Old Trafford buga tamaula.

Kulob din Sporting yana son a kammala komawar Nani kungiyar, kafin ta amince ta sayarwa da United Rojo kan kudi fam miliyan 13.

Haka kuma United ta karyata rahotannin da ake yadawa cewar tana zawarcin dauko 'yan kwallon Jamus Thomas Muller da Marco Reus.

Nani ya koma United ne a shekarar 2007, ya lashe kofunan Premier hudu da kofin zakarun Turai.