Ina shaukin buga wasa — Suarez

Luis Suarez
Image caption Suarez na shaukin ya buga wa Barcelona tamaula

Sabon dan kwallon Barcelona Luis Suarez ya ce yana shaukin buga wasa, tun lokacin da ya fara buga wa kulob din wasan sada zumunci da Leon ranar 18 ga watan Agusta.

Dan kwallon ya koma buga tamaula bayan da kotun daukaka karar wasanni ta yanke hukuncin zai iya buga wasan sada zumunci da yin atisaye da kuma yiwa kamfanoni tallace-tallace.

Suarez ya ce "Ina shaukin bugawa Barcelona wasanni, musamman tare da abokan wasa na domin ciyar da kungiyar gaba".

Dan kwallon ya buga wasan minti 15 a karawar da suka yi da Leon a wasan sada zumunci na cin kofin Joan Gamper.

A karawar Barcelona ce ta zura kwallaye 6-0, inda 'yan wasa Messi da Sandro da da Munir El Haddadi da kuma Neymar ne suka zura kwallayen.