Kenya ta nada Williamson kocinta

Bobby Williamson Hakkin mallakar hoto Andy Gooch
Image caption Tsohon kocin Uganda ya amince zai horas da Kenya

Hukumar kwallon kafar Kenya ta ba da sanarwar nada Bobby Williamson a matsayin sabon kocin tawagar 'yan kwallon kasar.

Mai shekaru 53 da haihuwa, ya shaida wa BBC cewa ya rattaba hannu kan kwantiragi da Kenya, amma zai jagoranci kulob dinsa Gor Mahia wasan na karshe da zai yi a karshen mako.

Tsohon kocin Uganda ya ce ya amince da kwantiragin da Kenya ta ba shi, bayan ya yi dogon nazari da kunshin data kunsa.

Shi ma kulob din Gor Mahiya ya sanar ta shafinsa na Intanet cewa kocinsa dan kasar Scotland zai tafi bayan wasan ranar Lahadi.

Williamson ya koma kungiyar ne a tsakiyar kakar wasan bara, inda ya taimaka wa kulob din lashe kofin Premier karo na 13.