'Ba na da-na-sanin rashin daukar Fabregas'

Cesc Fabregas Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wenger ya ce bai ji dadi da Fabregas ya bar Arsenal ba

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce bai yi dana sanin kin sake daukar Cesc Fabregas a kakar wasan bana ba.

Dan kwallon Spaniya mai shekaru 27, ya taka rawar gani a wasan farko da ya bugawa Chelsea lokacin da suka doke Burnley da ci 3-1 ranar Litinin.

Arsenal na da zabin sake sayo Fabregas a kunshin kwantiraginsa lokacin da ya koma Barcelona a shekarar 2011.

Wenger ya ce "Ko kadan ban yi da-na-sanin rashin sake dauko dan kwallon ba, illa na yi takaicin barinsa kungiyarmu tun farko".

Fabregas wanda ya bugawa Gunners wasanni 305, ya koma Chelsea ne kan kwantiragin shekaru biyar, bayan shekaru uku da ya bugawa Barca tamaula.