Atletico Madrid ta dauki Super Cup

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan wasan Atletico Madrid na murnar daukar kofin da kocinsu Diego Simeone

Zakarun gasar La Liga ta Spaniya Atletico Madrid sun dauki kofin zakaru na kasar bayan sun doke Real Madrid 1-0, jumulla 2-1 wasa gida da waje.

Wasan da aka yi a gidan Atletico shi ne karo na biyu bayan da a karon farko a gidan Real suka tashi 1-1.

Tsohon dan wasan Bayern Munich, Mario Mandzukic shi ne ya ci wa Atletico kwallon a minti biyu da fara wasa.

Wannan ya zama kofin farko na kakar bana da Atletico ta fara dauka bayan ta doke manyan abokan hamayyar tata.

Karin bayani