Samaras ya shiga West Brom

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Samaras ya je gasar cin kofin duniya na Brazil a bana, inda ya fitar da kasarsa kunya

Tsohon dan wasan gaba na Celtic Georgios Samaras, mai shekaru 29, ya sanya hannu a kan kwantiragin shekaru biyu da kungiyar West Brom.

Dan wasan na kasar Girka shi ne mutum na tara da West Brom ta dauka a bana.

Sai dai kungiyar ba ta bayyana a kan ko nawa ta sayi dan wasan ba.

Kocin West Brom Alan Irvine ya ce dan wasan ya buga kwallo a manyan gasa na duniya, ciki har da gasar zakarun Turai da gasar cin kofin nahiyar Turai har ma da kofin duniya.