Afcon 2017: Libya ta ce a kai kasuwa

afcon
Image caption Yakin basasa da ake a kasar ne ya hana Libya ci gaba da shirin karbar bakunci

Libya ta tsame hannunta a shiriye-shiryen karbar bakuncin gasar cin kofin Nahiyar Afirka na shekarar 2017, saboda tashin hankali da ake a kasar da ya hana gina sababbin filayen wasa.

Hukumar kwallon kafar Afirka CAF na zawarcin kasashen da ke sha'awar karbar bakuncin gasar, da su mika takardun sha'awarsu kafin karshen watan Satumba.

Tun a shekarar 2013 a ka tsara cewa Libya ce za ta karbi bakuncin gasar, amma saboda yakin basasar kasar yasa aka dage zuwa 2017.

CAF ta tsaida 20 ga watan Satumba domin fidda kasar da za ta karbi bakuncin gasar ta 2019 da 2021 a taron da za ta gudanar a Addis Ababa.

Kasahen da suke zawarcin karbar bakuncin gasar sun hada da Algeria da Cameroon da Guinea da Ivory Coast da kuma Zambia.