Barcelona ta doke Elche 3-0 a La Liga

Lionel Messi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Barcelona ta fara gasar La Ligar bana da kafar dama

Kulob din Barcelona ya fara gasar cin kofin La Ligar Spaniya na bana da kafar dama bayan da ya doke Elche da ci uku da nema a karawar da su kayi ranar Lahadi.

Lionel Messi ne ya fara zura kwallo a ragar Elche ya rage saura mintina uku a tafi hutun rabin lokaci, sai dai an bai wa Javier Mascherano jan kati bisa ketar da ya yiwa Garry Rodrigues.

Munir wanda ya fara bugawa Barca wasa ya buga kwallo ta bugi tirke, kafin ya samu dama a minti na 46 ya kuma zura kwallo a raga

Messi ne ya kara kwallo ta uku a raga bayan da ya yanke masu tsaron baya su uku a dai-dai minti na 63.

Barcelona za ta ziyarci Villareal a wasan mako na biyu ranar Lahadi.