Ebosse ya mutu da aka jefe shi a ka

Albert Ebosse
Image caption Dan kwallon shi ne jagaba a yawan zura kwallo a raga

Dan kwallon Cameroon Albert Ebosse ya mutu bayan da wani magoyin bayan kulob din hamayya ya jefe shi a kansa lokacin da suka ta shi wasa a Algeria.

An bada sanarwar mutuwar Ebosse mai shekaru 24 bayan da aka garzaya da shi wani asibitin da ke Tizi Ouzou a babban birnin Algiers.

Dan wasan JS Kabylie wanda ya zura kwallo a karawar da suka yi da USM Alger in da aka tashi wasa 2-1, ya gamu da ajalinsa ne lokacin da magoya baya suka fara jifansu daf da za su koma dakin hutun 'yan wasa bayan kammala kwallo.

Ebosse shi ne ke kan gaba wajen cin kwallaye a gasar cin kofin Algeria inda ya zura kwallaye 17 a raga.

Kungiyar USM Alger ta ce ta firgita da mutuwar Ebosse wanda ta bayyana a matsayin wani babban rashi.