Di Maria zai fi kowa tsada a Ingila

Angel Di Maria Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Di Maria ya yi ban kwana da 'yan wasa da jami'an Madrid

Kulub din Manchester United zai sayo dan wasan Real Madrid Angel Di Maria, a matsayin dan wasan da aka sayo mafi tsada a tarihin kwallon Ingila.

Kocin Madrid Carlo Ancelotti ya ce Di Maria mai shekaru 26 da haihuwa, ya yi bankwana da abokan kwallo da jami'ansa a shirin da yake na koma wa United.

An ce United ta taya dan wasan kan kudi fam miliyan 75 kan dan kwallon Argentina, kuma ba ta fatan farashinsa zai haura hakan.

United ta taba dauko dan kwallon baya Rio Ferdinan a matsayin wanda yafi tsada a gasar Premier daga kulob din Leeds kan kudi sama da fam miliyan 29 a shekarar 2009.

Ancelotti ya fada a ranar Lahadi ce wa "Di Maria ya yi atisaye da 'yan wasa da safe daga baya ya dawo yin bankwana da 'yan wasa da kuma jami'an Madrid".