Man United da Sunderland sun buga 1-1

Sunderland Team
Image caption Wasan da United ta buga 1-1 da Sunderland ranar Lahadi

Kulob din Manchester United ya tashi wasa 1-1 a gasar cin kofin Premier wasan mako na biyu da suka kara ranar Lahadi.

United ce ta fara zura kwallo a ragar Sunderland, ta hannun Juan Mata lokacin da ya samu kwallo daga bugun kusurwa da Antonio Valencia ya bugo kwallo a minti na 17 da fara wasa.

Sunderland ta farke kwallonta ta hannun Jack Rodwell da ya sa mata kai daga bugun kusurwa, saura mintuna 15 a tafi hutun rabin lokaci.

United ta buga wasanni biyu tana da maki daya a matsayi na 13 a teburin Premier, za kuma ta ziyarci Burnley a wasan mako na uku ranar Asabar.

Sunderland tana matsayi na 11 a teburin Premier da maki biyu, za kuma ta ziyarci Queens Park Rangers ranar Asabar.