Ebosse: An tsaida tamaula a Algeria

Albert Ebosse Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption CAF ta bukaci da a gudanar da binciken kan mutuwar dan kwallo

Kasar Algeria ta dakatar da tamaula nan take sakamakon mutuwar dan kwallon Cameroon Albert Ebosse, bisa jifansa da aka yi a ka.

Hukumar kwallon kafar Algeria ta yanke hukuncin hakanne bayan taron da ta gudanar ranar Lahadi.

Ebosse, mai shekaru 24, ya mutu ne lokacin da aka jefe shi a kansa daf da za su koma dakin hutun 'yan wasa bayan da kulob dinsa JS Kabylie ya doke USM Alge da ci 2-1 ranar Asabar.

Tuni mahukuntan Algeria suka bada dokar rufe filin wasa na 1st November 1954, wanda aka buga wasan a ciki da dukkan filayen wasan kasar.

Haka kuma hukumar kwallon kafar Algeria za ta bai wa iyalan Ebosse kudi dalar Amurka 100,000, sannan yan kwallon JS Kabylie za su taimakawa iyalan da albashinsu na wata daya.