Simeone: Da kyar mu kare kambunmu

Diego Simeone Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Kocin ya ce da kyar ne idan za su iya kare kambunsu

Kocin Atletico Madrid Diego Simeone ya ce da kyar ne idan za su iya hana daya daga cikin Real Madrid ko Barcelona lashe kofin La Ligar Spaniya a kakar bana.

Atletico ta dauki kofin La Liga a bara, wanda rabonta da kofin tun shekarar 1996, bayan da suka tashi wasa kunnen doki a karawar wasan karshe a bara.

Tun daga lokacin ne kulob din ya sayar da manyan 'yan wasansa, amma ya lashe Super Cup na Spaniya bayan da ya doke Real Madrid a bana.

Kocin ya ce "Za ka iya samun nasara a wasa daya zuwa biyu, amma da wuya ka dore da samun nasarori tsawon shekara guda sai ka yi da gaske".

Atletico Madrid za ta fara kare kambunta inda za ta kara da makwabciyarta Rayo Vallecano ranar Litinin.