Everton na daf da daukar Eto'o

Samuel Eto'o
Image caption Eto'o kasar Cameroon ba ta gayyace shi wasa ba

Kulob din Everton na daf da daukar dan kwallon Cameroon Samuel Eto'o kan kwantiragin shekaru biyu.

Tun farko Liverpool ta yi sha'awar dauko dan wasan mai shekaru 33, wanda kwantiraginsa ya kare da kulob din Chelsea a bara.

Daukar Balotelli da Liverpool ta yi kan kudi fan miliyan 16 ne ya bai wa Everton damar shiga zawarcin dan kwallo.

Everton na tattaunawa da Eto'o, wanda ta ke fatan kammala yarje-jeniya da shi, domin ya buga mata karawar da za ta yi da Chelsea a wasan hamayya ranar Asabar.

Everton ta dauko Romelu Lukaku kan kudi fan miliyan 28 daga Chelsea a bana, sannan ta karbi aron dan wasa Christian Atsu.