Van Gaal: Maki daya wasa 2 matsala ce

Van Gaal Puyot Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin ya ce United za ta dawo da tagomashinta a bana

Kocin Manchester United Louis van Gaal ya ce samun maki daya a wasa biyu da suka buga a gasar kofin Premier matsala ce da ba zai amince da ita ba.

Van Gaal ya fara wasan Premier bana da rashin nasara a gida inda Swansea ta doke su da ci 2-1.

Kocin ya ce "Yanzu muna da maki daya a wasanni biyu da muka buga, wanda bai da ce da kulob kamar United ba".

Har yanzu akwai jan aiki a gabanmu, yan wasa na sun yi takaicin kasa lashe Sunderland, domin tun farko mun ayyana cewa za mu doke su.

Da aka tambaye shi ko yaushe ne tagomashin kungiyar zai dawo, sai yace da zarar sun fara lashe wasanni.