Kamaru ta cire Eto'o a matsayin Kaftin

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rashin tabuka wani abin kirki da 'yan wasan Kamaru suka yi a Brazil ya janyo zargin aikata cogen wasa

Kamaru ta cire fitaccen dan wasanta Samuel Eto'o daga mukamin kaftin din kungiyar kwallon kafar kasar, inda ta maye gurbinsa da dan wasan tsakiya Stephane Mbia.

Hukumar kwallon kafar Kamaru ce ta sanar da wannan shawara ta karbe mukamin kyaftin daga hannun Eto'o, wanda da ma kocin kasar Volker Finke bai sanya shi cikin 'yan wasan da za su wakici kasar a wasannin samun cancantar shiga gasar cin kofin Afirka a watan gobe ba.

Hakan wata manuniya ce da ka iya kawo karshen zaman Eto'o mai shekaru 33 a kungiyar kwallon kafa ta Kamaru.

Kungiyar Kamaru ba ta ji dadi ba a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a Brazil karkashin jagorancin Eto'o, inda ta gaza lashe ko guda daya a cikin wasanni uku da ta buga, mafi muni ma shi ne wasan da Croatia ta lallasa ta da ci 4 da nema