Everton ta dauko Samuel Eto'o

Samuel Eto'o
Image caption Dan wasan zai buga wa Everton tamaular shekara biyu

Kungiyar Everton ta kammala cinikin Samuel Eto'o, wanda ya rattaba kwantiragin shekaru biyu, bayan da su kayi hannun riga da Chelsea a kakar bara.

Dan wasan Kamaru mai shekaru 33, ba shi da kwantiragi da kowacce kungiya, zai kuma buga wasa da Romelu Lukaku wanda Everton ta dauko daga Chelsea kan kudi fan miliyan 28 a bana.

Kocin Everton Roberto Martinez ya ce "Na tattauna da dan wasan, inda na yi farin ciki da yadda na fuskanci har yanzu yana da kishirwar zura kwallo a raga".

Kwantiragin Eto'o da Chelsea ya kare ne a karshen watan Yuli, wanda koci Jose Mourinho ya ki ya tsawaita kwantiragin dan wasan.

Tun farko Liverpool ce ta fara zawarcin dan wasan, kafin daga baya ta dauko Mario Balotelli, dalilin da Everton ta samu damar daukar dan kwallon.