Arsenal na jiran sakamakon raunin Giroud

Image caption Wenger ya ce ba shakka za su yi bakin ciki sosai idan karyewa dan wasan ya yi

Arsenal tana dakon sakamakon hoto na biyu da aka dauki dan wasanta na kasar Faransa, wanda ake fargabar cewa yana iya tafiya jinya tsawon watanni uku bayan raunin da ya ji a karawar kungiyarsa da Everton inda aka tashi 2 da 2.

Kocin kungiyar, Arsene Wenger ya ba da tabbacin cewa Giroud ba zai buga karawar da kungiyar za ta yi da Besiktas a ranar laraba don samun gurbi a gasar zakarun Turai ba.

Dan wasan mai shekaru 27 zai ga wani kwararren likita da zai tantance tsananin raunin da ya ji.

Rashin Giroud ya bar Arsenal da zabin sauran 'yan wasanta na gaba da suka hadar da Alexis Sanchez, Joel Campbell, Yaya Sanogo da Lukas Podolski