Arsenal ba za ta dauko dan wasan gaba ba

Oliver Giroud Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsenal ba ta shirin dauko dan wasan gaba a bana

Kungiyar Arsenal bata shirin dauko dan wasa mai zura kwallo a raga da zai maye gurbin Olivier Giroud, ko da sakamakon raunin da dan wasan ya ji ya yi muni.

Kulob din ba ya tunanin zawarcin dan wasan gaba da zai zauna din-dinnin a kungiyar a bana kafin rufe kasuwar musayar 'yan kwallo.

Wenger zai yi amfani da 'yan wasan da yake da su da suka hada da Alexis Sanchez da Joel Campbell da Yaya Sanogo da Lukas Podolski da kuma Theo Walcott.

Oliver Giroud mai shekaru 27, likitoci za su auna girman raunin da ya ji a karawar da su kayi da Everton su ka tashi wasa 2-2.

Sai dai Arsenal na fatan dauko dan wasa mai tsaron baya ko mai buga tsakiya wanda zai iya buga bangarorin biyu a lokaci daya, da zai dunga wasa a jiran kar ta kwana.