Taron NFF an tashi baram-baram

Hakkin mallakar hoto getty
Image caption Hukumar tsaro ta SSS ce ta gayyaci Maigari

Taron hukumar kwallon kafar Nageria NFF ya tashi baram-baram, bayan da aka gudanar da zabe cikin takaddama da ya raba kan mambobin hukumar zuwa gida biyu.

Shugaban hukumar mai barin gado Aminu Maigari ne ya kamata ya jagoranci taron, da nufin tsara yadda za a gudanar da zaben sabbin shugabannin hukumar.

Sai dai Aminu mai gari bai halarci wurin taron ba tare da sakataren tsare-tsaren hukumar Musa Amadu, saboda jami'an tsaro sun gayyace su amsa tambayoyi a offishinsu.

Rashin halartar shugaban wajen taro yasa aka zabi Chris Giwa a matsayin sabon shugaban hukumar da goyon bayan ministan wasanni na kasar.

Sai dai wasu tsagin mambobin hukumar sun gudanar da taronsu daban, wanda ba su amince da zaben da aka gudanar ba, har ma suka tsaida ranar 4 ga watan Satumba ranar da za a zabi sabbin shugabannin hukumar.

Wannan rikita-rikitar ta yi karo da umarnin Fifa a wasikar da ta turawa NFF a makon jiya, inda ta ce ta amince a gudanar da taron da zai tsaida ranar da za a gudanar da zaben sabbin Shugabanni.

Image caption Taron dai ya gamu da cikas, inda mambobin hukumar su ka rabu gida biyu

Barkewar wannan rikicin ya jefa Nigeria cikin tsaka mai wuya, domin FIFA za ta iya dakatar da kasar shiga harkar kwallon kafa, saboda tsoma hannun gwamnati cikin harkokin hukumar kwallon kafar kasar.

Sau biyu mambobin NFF suna dakatar da Aminu Maigari daga kan kujerarsa, wanda sakamakon hakan FIFA ta dakatar da Nigeria shiga harkar tamaula har sai da aka maida shi kan aikinsa.