'Ramirez da Jack ba na aro ba ne'

Ronald Koeman Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Koeman ya ce 'yan wasansa ba na sayarwa ba ne

Kocin Southampton Ronald Koeman, ya bayyana cewa ba zai ba da aro ko kuma sayar da 'yan wasansa biyu Gaston Ramirez da Jack Cork ba.

Ana dai danganta dan wasan gaba Ramirez da ba da shi aro na tsawon lokaci ga kulob din Sevilla yayin da shi kuma Cork ya koma Crystal Palace amma duk da haka Koeman ya rike su.

Kocin ya kuma ce suna bukatar dukkanin 'yan wasansu, inda ya kara da cewa "tawagarmu ba ta yi karfin da za ta fara tunani ba da aron 'yan wasa ba."

Kocin dan kasar Holland, na fatan kara sayen wasu 'yan wasa kafin lokaci ya kure.